24 Nuwamba 2026 - 08:36
Source: ABNA24
Libya: Harin Ukraine A Tashar Jiragen Ruwa Ta Benghazi Buga Gangar Yaƙi Ne

Manyan jami'an Libya, yayin da suke kwatanta harin Ukraine a tashar jiragen ruwa ta "Benghazi" a matsayin busa kahon yaƙi, sun ce wasu ɓangarori suna ƙoƙarin jawo Libya cikin yaƙe-yaƙen Ukraine da Sudan.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Da sanyin safiyar Litinin ne sojojin Ukraine, ta hanyar amfani da jiragen ruwa marasa matuki, suka kai hari ga wani jirgin ruwan yaƙi da wani jirgin ruwan dakon kaya na soji na Rasha a tashar jiragen ruwa ta Benghazi, inda suka nutsar da su.

Ta dalilin hakan Libya na shirin mika fayil ɗin harin ta'addanci a tashar jiragen ruwa ta Benghazi, wanda a cewar rahoton da aka wallafa, Ukraine ta ɗauki alhakinsa, ga kotun shari'a ta ƙasa da ƙasa ta Majalisar Dinkin Duniya.

Musa Al-Koni, mataimakin shugaban majalisar shugabancin Libya, ya buƙaci a sanya sunan Volodymyr Zelensky, shugaban Ukraine, cikin jerin 'yan ta'adda.

Al-Koni ya kuma buƙaci a gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa game da wannan hari da kuma nazarin fagagen da bangarorin da ke da hannu a ciki.

……..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha